Connect with us

Hausa

Za a samar da maganin HIV mai ɗanɗanon inibi ga yara a Afirka

Published

on

Magani

Hukumomin agaji sun ce za a samar da magani mai ɗanɗanon itacen inibi mara tsada ga yaran da suke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a Afirka a shekara mai zuwa.

Za a samar da maganin ne har ma ga jariran da suke ɗauke da cutar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa a cikin yara fiye da miliyan ɗaya da rabi dake ɗauke da ƙwayar cutar a duniya, rabinsu ne kaɗai ke iya samun magani.

Wani abu da ke hana yaran da suke ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki su sha maganin cutar shi ne saboda rashin daɗinsa ga kuma ɗaci.

Kwararru a fannin lafiya sun ce samar da maganin HIV ɗin ga yara mai ɗanɗanon inibin, zai matukar taimakawa yaran su rinƙa sha ba tare da damuwa ba.

A cewar ƙwararru nan da wasu watanni masu zuwa yaran da suke a ƙasashen Benin da Kenya da Malawi da Najeriya da kuma Zimbabwe za su samu irin wannan magani na cutar ta HIV mai dandanon inibi.

Karin bayani

Masana kiwon lafiya dai na kara nanata cewa idan mutum ya kamu da cutar HIV, to ba shi ne karshen rayuwarsa ba, domin akwai maganin da ake sha, wanda idan har mutum ya kiyaye da ka’idar maganin to ba lallai ne idan aka ganshi ace ma yana da cutar ba.

Shirin haɗin gwiwa kan yaƙi da HIV da AIDS na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙiyasin mutum miliyan 38 ne ke fama da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki a duniya, kuma sama da miliyan 35 ne suka mutu tun fara gano cutar a 1984.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending