Jam’iyar APGA ta lashe zaɓen dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 na jihar Anambra.
A ranar Asabar ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Anambra ANSIEC ta gudanar da zaɓe a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.
A wannan ne karo na farko da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar tun shekarar 2013.
Kafin wannan lokaci jam’iyar APC da kuma Labour Party sun bayyana damuwarsu kan zaɓen a yayin da wasu jam’iyun suka ƙauracewa zaɓen.
Da take gabatar da sakamakon zaɓen a Awka babban birnin jihar a ranar Lahadi, Genevieve Osakwe shugabar hukumar zaɓen jihar ta ce APGA ta lashe zaɓen a ƙananan hukumomi 21 da kuma mazaɓu 326 a jihar.
Da take mayar da martani kan sakamakon jam’iyar APGA ta ce sakamakon ya nuna irin ƙarfin da jam’iyar take da shi a jihar.