APC ta ki amincewa da matakin INEC kan zaben Bauchi

APC
Hakkin mallakar hoto
APC
Image caption

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana matakin da hukumar INEC ta dauka kan sakamakon zabuka jihohin Bauchi da Ribas a zaman wanda ya saba wa doka.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin lahadi, jam’iyyar ta ce ta yi fatali da amincewar da hukumar ta yi da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

Shugaban jam’iyyar reshen jihar Bauchi Alhaji Ahmad Uba Nana ya shaidawa BBC cewa hukumar zabe ba ta da hurumin yin amai ta lashe musamman la’akari da cewa maganar da gaban kotu.

Alhaji Uba ya ce ba za su lamunci matsayin INEC ba, domin kowa ya shaida abin da ya faru a karamar hukumar Tafawa Balewa da kura-kuran da aka samu.

Daga cikin dalilan da jam’iyyar ta bayar har da zargin cewa akwai alaka tsakanin wanda hukumar ta tura domin tantance gaskiyar abin da ya faru a yanki wato Festus Okoye da kuma Kakakin majalisar wakilan kasar Yakubu Dogara wanda dan jam’iyyar PDP ne kamar yadda Alhaji Ahmad Uba ke cewa.

To sai dai a bangare guda jam’iyyar PDP wadda ke kan gaba a zaben na jihar Bauchi ta ce matakin hukumar ya yi mata daidai.

Jam’iyyarta bayyana haka ne duk da cewa da farko ta shigar da kara kotu ta na kalubalantar ayyana sakamakon zaben jihar a zaman wanda bai kammala ba da INEC ta yi da farko.

A tattaunawarsa da BBC shugaban jam’iyyar ta PDP a Bauchi Hamza Koshe Akuyam ya ce dama an riga an yi zabe kuma korafin da aka shigar an warwareta.

Hamza Koshe ya ce dama a duk lokacin da za a zalunce ka, kana da damar rugawa wurin alkali ka bi hakkin ka, kuma dama su ba wai sun ki a sake zaben ba ne abin da suke so shi ne INEC ta saurare su.

Ya kuma kara da cewa hukumar zabe ta gane cewa ta yi kuskure shi ne ya sa ta ce a kammala karbar sakamako da bayyana wanda ya yi nasara.

Hamza ya ce ba wai sun goyi bayan hukumar zabe don suna ganin za su iya nasarar ba ne, sai dai kawai suna ganin matakinta shi ne daidai la’akari da cewa ba a samu hatsaniya a mazabar da a baya ake tunanin sake zaben ba.

A gobe Talata INEC ta ce za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na mazabu da rumfunan zabe domin hada sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki na jiha.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...