Ana yada karya da sunanmu game da zaben Kano, inji BBC

A yakin da BBC ta ke yi da yada labaran boge, kafar ta gano wani shafi da aka bude da sunan ”Bbc hausa nigeria” a shafin Facebook inda shafin ke karkatar da hankulan jama’a zuwa ga labarun karya da sunan kafar BBC Hausa.

Akwai irin wadannan shafukan a kafafen sada zumunta na Intanet da dama, masu yada labaran karya da sunan BBC Hausa.

Wani labari da irin wadannan shafuka na boge suka buga shi ne labarin da aka alakanta sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso yana zagin wasu ‘yan siyasa da masu sarauta na jihar Kano.

BBC Hausa ta nisanta kanta daga wannan labarin da kuma makamantansu a irin wadannan shafukan na boge.

Shafin BBC Hausa na ainahi ya fita daban kuma za a ga alamar maki shudi a gefen shafin daga hannun hagu kamar haka:

Wata alama da za a kara tabbatar da shafin BBC Hausa na ainahi za a ga cewa akwai sama da mutum miliyan biyu da suke bin wannan shafi.

Shima shafin BBC Hausa na Twitter za a ga alamar maki shudi a gefen shafin daga hannun hagu kamar haka;

Hakazalika shafin Twitter na BBC Hausa za a ga sama da mutane dubu 60 ne ke bin wannan shafin

Yada labaran boge ba sabon abu ba ne musamman a shafukan sada zumunta.

Akan yi amfani da shafuka irin su Facebook da Twitter domin yada irin wadannan labaran.

Manyan kafafen yada labarai a fadin duniya irin su BBC sun dade suna wayar da kan jama’a a kan irin yadda ake gane labarun boge da shafukan boge.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...