Ana matsanancin sanyi a Amurka

Workers remove ice from an aeroplane in Chicago, which is expected to be one of the worst affected cities

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Amurka na fama da wani matsanancin sanyi wanda aka shafe gomman shekaru ba a taba samun irinsa ba.

Ban da tsananin sanyi, akwai wata iska mai karfi daga yankin Arctic na arewacin duniya da ka iya kawo matsanancin sanyi na kasa da ma’aunin Celsius -53.

Jami’ai a jihar Iowa na gargadin mutane da su guji shakar numfashi mai yawa, kuma su rage yin magana idan sun fita wajen gidajensu.

Akalla mutum miliyan 55 ne ake sa ran yanayin matsanancin sanyi zai shafe su.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ayyana dokar ta baci a jihohin Wisconsin da Michigan da Illinois

An ayyana dokar ta baci a jihohin tsakiyar Amurka kamar Wisconsin da Michigan da Illinois, har ma da jihohin da ke kudancin kasar kamar Alabama da Mississippi.

John Gagan, wani jami’in hukumar da ke kula yanayi na Amurka ya ce irin wannan tsananin sanyin na zuwa ne sau daya a gomman shekaru.

Ana kuma hasashen sanyin zai cigaba da karuwa har ranar Alhamis, jami’ai sun ce sanyi a birnin Chicago zai zarce na yankin Antarctica.

An dai soke fiye da sauka da tashin jiragen sama 1,100 daga ciki da wajen Amurka tun jiya Talata.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An umarci masu mota su kiyaye a lokacin wannan matsanancin sanyin

Lamarin ya kai har hukumomi a yankin tsakiyar Amurka an rufe dubban makarantu da shaguna har ma da ofisoshin gwamnati.

Sannan hukumomin sun samar wa mutanen da ba su da wurin zuwa wuraren da za su fake daga wannan matsanancin sanyin a biranen Amurka da dama har da jihar Milwaukee.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...