Ana ci gaba da zanga-zanga a wasu biranen Sudan

Shugaba al-Bashir ya yi shekara 30 a mulki

Shugaba al-Bashir ya yi shekara 30 a mulki

Bangarori biyu da ke adawa da juna sun yi tattaki a titunan Khartoum, babban birnin Sudan da birnin Omdurman.

Daruruwan mutane ne suka taru a dandalin Green Square don jaddada goyon bayansu ga Shugaba Omar al-Bashir, wanda ke fuskantar kalubale mafi girma a shekaru 30 da ya yi a mulki.

Taron mutanen, wanda yawanci ‘yan jam’iyya mai mulki ne da ma’aikatan gwamnati sun taru don karfafa wa shugaban mai shekaru 76 gwiwa.

Wannan ne jawabin farko da shugaban ya yi a bainar jama’a a Khartoum tun fara zanga-zangar kin jinin gwamnati a garin Atbara da ke arewacin kasar ran 19 ga watan Disamba.

Shugaban ya bayyana ne da matarsa Wedad Babkier, inda ta tsaya daga bayansa.

Ya yi zargin cewa wasu ‘yan tada zaune tsaye daga wajen kasar ne ke shirya zanga-zangar, kuma ya yabi rundunar soji da sauran jami’an tsaro kan kokarinsu a yayin zanga-zangar.

A daya bangaren kasar kuwa a birnin Omdurman, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati mafi girma a kasar.

A watan da ya gabata ne dai aka fara zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin inda har likitocin kasar ma suka shiga zanga-zangar .

Masu zanga-zangar sun kona ofishoshin jam’iyya mai mulki da wasu hukumomin gwamnati.

Kawo yanzu, a kalla mutane goma aka kashe.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...