An yi sata wa Karim Benzema

Karim Benzema playing for Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Yawan wadanda iftila’in ya shafa na karuwa amma kuma salon aikata ta’adar na nan yadda yake.

Suna jira ne har sai dan kwallo ya bar gida a lokacin babban wasa, sai su ‘balla kofa su yashe shi.

Mutum na kwanan nan da aka yiwa sata a ‘yan kwallon duniya shine Karim Benzema, wanda aka balla gidan sa ran laraba yayin da yake tsaka da bugawa Real Madrid wasa a karawa ta biyu da Barcelona a wasan daf da na karshe na gasar copa del rey.

Wani dare ne da dan wasan gaban kasar faransan ba zai manta da shi ba bayan da ya kasa taimakawa kungiyar tasa ta kare kanta daga shan kashin da ta yi 3-0 a hannun kungiyar ta katolika wacce ta yi waje rod da su daga gasar.

Makonni biyu da suka gabata irin wannan iftila’in ya fadawa Kevin-Prince Boateng, wanda Barcelona ta saya a watan Janairu, wanda aka yiwa sata yana tsaka da buga wasan su da Valladolid a gasar kasar Spain.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Haka shima abokin taka ledar sa Jordi Alba bai tsira ba, inda aka tafka masa sata a watan Nuwambar bara.

A lokacin da abin ya faru suna Milan don wasa da Inter Milan a gasar zakarun Turai, kawai sai barayi suka haura gidan sa, sannan suka balla masa akwatin ajiye kud’i.

A Faransa

Wannan matsalar ba wai a Spain kawai take faruwa ba, hakika ‘yan wasa hudu aka yiwa sata a faransa a makon da ya gabata.

Kamar yadda ofishin shigar da ‘ara na Nanterre dake cikin birnin Paris ya baiyana ran Lahadi, ya ce an haura gidan dan kasar Brazil Dani Alves aka yi masa sata lokacin yana tsaka da wasan da PSG ta kara da Montpellier a filin wasa na Parc de Princes dake babban birnin kasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Haka kuma jaridar nan ta L’Equipe ta ruwaito cewa barayin sun kwashi abubuwa masu daraja da kuma dubban daloli.

Haka kuma, an yashe ‘yan wasan Lyon Memphis Depay da Lucas Tousart da Pape Cheikh Diop yayin da suke tsaka da karawa da Barcelona a gasar zakarun turai ranar talata.

Wannan ya faru ne bayan da aka haura gidan Shugaban Marseille, Jacques-Henri Eyraud da na ‘yan wasan Paris Saint-Germain Eric Maxim Choupo-Moting har sau biyu a watannin Nuwamba da Disambar bara, da kuma gidan Thiago Silva shima a watan Disambar bara.

A Ingila

Wannan ta’asar ta balla gidajen yan kwallo yayin da suka fita wasa ba sabon abu bane kuma matsala ce da ke ci gaba da karuwa a arewa maso yammacin ingila.

Misali, tsakanin 2006 da 2009, ‘yan kwallo 21 aka haurawa gidaje a yankin.

Na farko da aka ruwaito shine na Sadio Mane dan kasar Senegal wanda aka kwashe masa agoguna, wayoyin salula da kuma mukullin motar sa lokacin yana wasa da Bayern Munich a gasar zakarun Turai a filin wasa na Anfield, kuma a daren ne aka tafka satar da aka yiwa ‘yan wasan Lyon.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mane, wanda ya taba gamuwa da iftila’in sata a 2017, ya shiga dogon jerin ‘yan wasa sama da ashirin a Liverpool da sauran kungiyoyi a yankin da aikata muggan laifuka ya shafa a shekaru goma sha biyar da suka gabata.

Haka Roberto Firmino, Steven Gerrard da Pepe Reina suka sha sata lokacin suna taka leda a Liverpool.

A wajen garin kuma akwai irin su Romelu Lukaku, Wayne Rooney da Roque Santa Cruz dan kasar Paraguay, wanda aka haura gidan sa aka yi masa sata yana tsaka da wasa a Blackburn Rovers.

Amma ba ko yaushe ne kakar barayin take yanke sa’ka ba.

A 2003, dan wasan Everton Duncan Ferguson ya kasance yana gida sai wani barawo mai suna Carl Bishop ya hauro yayi yunkurin sa ce masa tulun giya.

Lokacin da bishop yayi arba da Ferguson sai yayi yunkurin ya dokawa dan wasan kwalbar barasa a ka, amma sai Ferguson din ya naushe shi a fuska.

Saida zafin naushin ne yasa har sai da Bishop ya kwashe kwanaki biyu a gadon asibiti.

Wannan shine karo na biyu da Ferguson din ya dakile yunkurin yi masa sata a gida, inda a 2001 ne da aka yi yunkurin yi masa sata sai kawai ya kira ‘yan sanda a waya ya kuma yi nasarar zaune barawon har sai da ‘yan sandan suka zo.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...