An yi musayar wuta tsakanin ‘yan sa kai da masu satar mutane

Satar mutane da garkuwa da su don neman kudin fansa ta zamo ruwan dare a Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Daily Post Nigeria

Da alama matsalar tsaro a Najeriya ta fara kai talakawan kasar bango matuka saboda sun fara yin gangami suna shiga dazuka don farautar masu satar shanu da mutane suna garkuwa da su don neman kudin fansa.

Jama’a daga yankunan kananan hukumomin da ke makwabtaka da dajin Kamako ne suka yi wani gangamin sa kai inda suka hadu a gari Dungun Ma’azu da ke yankin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina inda suka shiga dajin domin kai wa maharan da ke addabar yankunansu samame.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa, mutane akalla sama da 500 daga kananan hukumomin Katsina da ma na Kaduna suka yi wannan gangami inda suka shiga wannan dajin.

Ganau din wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce an yi karan-batta sosai a tsakanin ‘yan sa kan da kuma masu satar mutanen.

Mutumin ya ce ‘ An kashe masu satar mutane akalla 40, yayin da aka kashe mutane ‘yan sa kan da suka shiga cikin dajin kuma 21’.

Ganau ya ce, wannan samame da mutanen garuruwan suka kai wa masu satar mutanen, ya yi matukar tasiri, saboda ko da aka koma a washegarin da aka yi wannan karan-battar ta farko, ba a samu kowa ba duk sun gudu.

Ya ce ganin hakan ya sa ‘yan sa kan suka kara damara inda har aka samu karuwar wasu mutane ma a cikinsu.

Ko me ya sa mutanen gari daukar wannan mataki?

Ganau din ya ce ‘ Jama’a sun ga hukumomi ba su dauki wani mataki ba a kan irin koke-koken da ake kai musu na satar mutane domin kudin fansa da kuma hare-haren da ake kai wa cikin kauyuka ana kashe mutane ba bu gaira ba bu dalili, wannan shi ya sa mutane suka dauki wannan mataki’.

Ya ci gaba da cewa, mutanen da suka dauki matakin sun lura da cewa idan har ba a magance wannan matsala ba, to noma ma zai gagare su, don haka suka hada kansu don shiga dajin.

Dajin Kamako dai babban daji ne wanda iyaka da Birnin Gwari da Zamfara da kuma jihar Neja.

Ko menene martanin hukumomi a kan wannan mataki na ‘yan sa kai?

BBC ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, SP Gambo Musa, wanda ya ce wannan mataki wani sabon salo ne da mutane ke yin gaban kansu.

SP Gambo, ya ce ‘yan sa kan ba daya suke da ‘yan kungiyar sintiri ba, kuma ba su da goyon bayan hukuma.

Daga bisani jami’in dan sandan, ya yi gargadi a kan cewa yakamata jama’a su guji irin aikata wannan gaban kai bisa la’akari da hadarin da ke tattare da shi.

SP Gambo ya ce, yakamata jama’a su sani cewa, rundunarsu tare da hadin kan sojoji na iya bakin kokarinsu wajen shawo kan wannan matsala ta satar mutane da kuma shiga cikin kauyuka ana kashe mutane ba bu laifin zaune balle na tsaye.

Karin bayani

Masu sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya dai na ganin cewa irin wannan kukan kura da jama’a suka fara yi suna shiga dazukan da maharan suke, wata alamace da ke nuna cewa hakika turar matsalar tsaro ta kai bango a Najeriya.

Don haka akwai bukatar hukumomi suka kara zage damtse don magance matsalar cikin gaggawa.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...