An yi garkuwa da ƴan jarida biyu tare da iyalansu a Kaduna

Ƴan fashin daji sun yi garkuwa da wasu ƴan jarida biyu da kuma iyalansu a jihar Kaduna.

Ƴan fashin dajin ɗauke da makamai sun farma unguwar Danhonu dake  sabon garin Kaduna na Millennium City dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

Maharan sun afka gidan Alhaji Abdulgafar Alebelewe wakilin jaridar The Nation da kuma Abdulawahab Aodu wakilin jaridar Blueprint.

Alebelewe shi ne shugaban ɓangaren masu ɗauko rahoto a ƙungiyar ƴan jaridu ta NUJ a jihar.

Taofeek Olayemi wanda  ɗan uwan ɗaya daga cikin mutanen da aka sace wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ƴan fashin dajin sun farma unguwar ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Asabar inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi kafin su aiwatar da abun da ya kawo su.

Ya ce sun yi garkuwa da Alhaji Alebelewe, matarsa da kuma ƴaƴansa biyu a yayin da aka ɗauke Alhaji Aodu da matarsa aka kuma bar ƴarsa da bata da lafiya.

More from this stream

Recomended