An samu biliyoyin kudade, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

[ad_1]








A wani rahoton da jaridar Newsbreakng ta wallafa a jiya asabar yace, an gano makudan kudade har Naira biliyan 21 a gidan tsohon shugaban hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Mallam Lawal Musa Daura dake babban birnin tarayya, Abuja.

Wata majiya dake da masaniya kan lamarin tayi ikirarin cewa an gano bindigogi sama da 4000 tare da wasu kananan makamai da kuma katin zabe mallakar wasu bakin haure daga jamhuriyar Nijar duk a gidan nasa.

Ana tuhumar tsohon shugaban DSS din da karkatar da wasu makuden kudade har dala milyan 21 da ya gada daga tsohon shugaban hukumar DSS, Mr Ita Ekpenyong.

A halin yanzu Daura na amsa tambayoyi game da kudin pansho N12.9 biliyan da aka fitar daga asusun ajiya ta hukumar na DSS.

Ana kuma tuhumarsa da hannu cikin cire N1.6 biliyan daga asusun ajiyar inshora na ma’aikatan hukumar, inji majiyar.

Sai dai babu wata kwakkwarar majiya daga hukumar data tabbatar da afkuwar wannan lamarin saboda babu wanda yake son yin tsokaci akan wannan babban batu irin wanda daya shafi tsohon shugaban hukumar ta DSS.

A ranar Alhamis data gabata, tsohon shugaban hukumar DSS, Ekpenyong ya bayyana a hedkwatar hukumar EFCC inda ya amsa tambayoyi kan yadda ya sarrafa kudaden da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Kanal Sambo Dasuki, ya bashi gabanin zaben shekarar 2015.




[ad_2]

More News

Mutane 8 sun mutu a hatsarin mota akan hanyar Abuja-Lokoja

Fasinjoji 8 aka tabbatar sun mutu wasu biyu kuma suka jikkata bayan da wata motar fasinja Æ™irar  ta daki wata babbar mota a kusa...

Mutane 9 sun mutu wasu 3 sun jikkata a hatsarin mota a Kano

Mutanen da basu gaza 9 ne ba suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Kano zuwa Zaria a...

Ƴan bindiga sun nemi kudin fansa N30m da babura kan ɗan takarar kansila da suka sace a Kaduna

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani dan takarar kansila mai suna Japheth Zarma Yakubu a unguwar Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia...

Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari a Maiduguri

Ana fargabar tserewar fursunoni biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye gidan yari a birnin Maiduguri. Aƙalla fursunoni 200 ake kyautata zaton sun tsere daga...