Wasu sabbin ’yan daba 43 (Yan Daba) daga daga yankin Goburawa-Gangare da Tudun Fulani Quarters na karamar hukumar Ungogo ta Jihar Kano sun rungumi zaman lafiya tare da mika kansu ga rundunar ‘yan sandan jihar.
‘Yan barandan 43 sun sa adadin tubabbun ‘yan baranda a Jihar zuwa 143. ‘Yan barandan sun kasance tare da wasu dattijai, masu ruwa da tsaki a cikin al’umma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa wadannan ‘yan daba 43 na kungiyoyin biyu a baya sun yi artabu da juna (Fadan Yan Daba) sama da shekaru biyar.
Sanarwar ta ce, fadan ya kan kai ga kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wanda ke haddasa asarar rayuka, da jikkatar mutane, da kuma asarar dukiyoyi.