An naɗa sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bauchi

Gwamnatin Najeriya ta naɗa Sani Usman a matsayin babban shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bauchi a jihar Bauchi.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ne dai ya mika wasikar nadin wa sabon wanda aka nada ɗin.

Har zuwa lokacin da aka nada shi a halin yanzu, Mista Usman ya kasance mataimakin shugaban makarantar ne, mukamin da ya rike daga 2018 zuwa 2022.Nadin, a cewar mataimakin magatakardar hukumar mai kula da hulda da jama’a, Muhammad Rabiu, ya fara aiki ne daga ranar 21 ga watan Mayu.Ya gaji Sanusi Waziri, wanda aka nada a watan Fabrairu, 2018.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...