Connect with us

Hausa

An kashe mutum 64 a Sokoto a mako guda, sama da mutum 100 cikin wata guda

Published

on

..

Asalin hoton, Sokoto State Government

Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta ce alƙaluman mutanen da aka kashe sanadin wani mummunan harin ƴan fashin daji a yankin ƙaramar hukumar Illela ya ƙaru zuwa mutum 43 hakazalika an tabbatar da kashe aƙalla mutum 21 a wani hari da aka kai yankin Sabon Birni duk a jihar ta Sokoto.

Tun da farko dai gwamnatin jihar ta ce mutum 13 aka kashe a ƙauyukan da ke cikin Illelah, sai mutum biyu a ƙaramar hukumar Goronyo sakamakon harin na wayewar garin ranar Litinin.

Sai dai a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Illelah a ranar Laraba, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya gano cewa munin harin ya wuce yadda aka yi ƙiyasi tun da farko.

A hira da BBC, mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai Muhammad Bello ya bayyana cewa tun da fari ƴan bindigar sun je ne bisa babura inda suka afka cikin ƙauyuka aƙalla guda bakwai sannan da cikin garin Illela.

Ya tabbatar wa BBC cewa ko da waɗannan ƴan bindigar suka kai hari akwai jami’an tsaro da kuma jami’an sa-kai.

Ya ce cikin waɗanda aka raunata har da wani dagacin ƙauye, sannan akwai waɗanda suke asibiti a kwance sannan akwai waɗanda suke jinya a gida.

A yankin sabon birni kuwa ƴan bindigar kan babura sun sace kayan abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum bayan kashe aƙalla mutum 21. Sun kai hare-haren ne a daren Talata inda harin ya fi munana a ƙauyen Sangerawa.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda reshen jihar Sokoto Sanusi Abubakar ya tabbatar wa BBC da batun kisan amma ya ce suna ci gaba da tattara bayanai.

Kashe mutum 49 a Goronyo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Ko a watan jiya ma, ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.

Ko a watan jiya sai da ƴan bindigar suka kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.

Waɗanda suka shaida lamarin sun tabbatar wa BBC cewa an ƙidaya gawa 49 yayin da mutum 17 suka jikkata inda gawarwakin aka kai su mutuwaren da ke babban asibitin garin Goronyo bayan faruwar lamarin.

Hakan na nufin cikin ƙasa da wata guda an kashe sama da mutum 100 a jihar ta Sokoto kaɗai.

Arewacin Najeriya dai na fama da hare-haren ƴan bindiga da na Boko Haram da ƙungiyar ISWAP, lamarin da ya ja asarar dubban rayuka da dukiyoyi.

Ana yawan caccakar hukumomi kan gazawa wajen shawo kan matsalar tsaro duk da cewa gwamnatin ƙasar tana tura dubban jami’an tsaro da kuma katse layukan sadarwa duk a yunƙurin kawo zaman lafiya a wasu sassa na yankin.

Ko a kwanakin baya sai da aka fitar da wani rahoto a Najeriyar inda rahoton ya ce a watan Oktoban 2021 kaɗai, an kashe mutum aƙalla 636.

Rahoton wanda kamfanin Beacon Consulting ya fitar, ya ce alƙalummansa sun shafi jihohi 33 na Najeriya a ƙananan hukumomi 105.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending