An kashe mutane 16 a harin da mayaƙan Boko Haram suka kai Yobe

Mutanen da basu gaza 16 ne ba aka kashe a yayin da wasu huɗu suka jikkata a wani harin da mayaƙan Boko Haram suka kai a ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.

Ƴan ta’addar sun farwa ƙauyen Nguro Kayayya dake wajen karamar hukumar ta Geidam da daddaren ranar Litinin lokacin da mutanen ƙauyen suke bacci.

Wani da yake da yan uwa a garin ya fadawa jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa shi da kansa da ya ƙirga gawarwakin mutane 16 bayan harin.

“Sun kai farmaki garin lokacin da mafi yawan mutane suna barci. Naje wurin da kai na inda na ƙirga gawarwaki 16 a yayin da mutane huɗu suka ji rauni. Su masu raunin na samun kulawa a asibitin kwararru dake Geidam.”

Ya ce ƴan ta’addar sun kai farmaki ƙauyen ne bayan da mazauna garin da yawancinsu manoma suka ƙi biyan harajin da ƴan bindigar suka saka musu.

A ƴan kwanakin nan dai ƙaramar hukumar Geidam na cigaba da fuskantar hare hare daga mayaƙan na Boko Haram.

More from this stream

Recomended