An kama samfurin kuri’u buhu bakwai a Jigawa

takardun zabe
Image caption

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa ‘yan sanda sun cafke wasu kuri’a na gwaji da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa.

Batun dai ya janyo takaddama tsakanin jam’iyyar PDP da ta APC kan abinda ake shirin yi da takardun.

Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama buhunhuna makare da takardun kada kuri’a na gwajin, da aka ce za a kai su jihar Jigawa ne da ke makotaka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano mohammad wakili shi ne ya yi min karin bayani kan takardun da aka kama.

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce tsakanin jam’iyyar PDP da APC a jihar Jigawa.

Ita dai PDP tana zargin cewa APC ce ta buga takardun a wani mataki na yunkurin magudi.

Shugaban kwamitin matasa na yakin neman zaben dantakarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jigawa, Umar Danjani ne ya shaida wa BBC hakan.

“Muna zargin APC ta shirya yin magudi a kananan hukumomi 17, kuma abun da ya ja hankalinmu shi ne ganin cewa buhunhuna 17 ne ‘yan sandan suka kuma,” in ji shi.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa matakin wani yunkuri ne na magudin zabe, kamar yadda kakakin jam’iyyar Nasir dahiru Jahun ya shaida wa BBC.

“Mun buga samfuri ne don wayar da kan masu zabe kamar yadda ita ma hukumar zabe karkashin jagorancin shugabanta na kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya tara ‘yan jaridu da shugabannin jam’iyyu ya yi musu karin haske kan yadda takardar kada kuri’a za ta kasance da kuma yadda za su wayar da kan mutanensu.

“Don haka wannan zargi ne mara tushe da makama, mu ba yunkurin magudi muka yi ba,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

To ko wake da alhakin buga wannan takardar wayar da kan masu zabe?

Tambayar kenan da BBC ta yi wa Garba Lawan mai magana da yawun hukumar zabe mai zaman kanta na jahar Kano.

Ya kuma ce: “Hukumar zabe ce ke da alhakin buga takardun da kuma masu sa ido kan zabe da jam’iyyu da al’ummar gari, amma ba ta yarda wani ya buga a karan kansa ba.”

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...