An kama ɓarayin wayoyin wutar lantarki a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu mutane uku da ake zargi da sace igiyoyin wutar lantarki a garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Kaduna.

Hassan ya ce da misalin karfe 0400 na ranar Lahadi, rundunar ta samu bayanai game da sace-sacen da aka yi a wani gida a kan titin Kafanchan, cikin garin Saminaka, an ga wasu da ba a san ko su waye ba dauke da wasu igiyoyin wutar lantarki.

“An kai tawagar mu ‘yan sintiri zuwa yankin, kuma an kama mutanen uku da suka fito daga Unguwar Ungwan Bawa na garin,” in ji shi.

More from this stream

Recomended