An kama ƴan ƙasashen waje dake ɗaukar nauyin masu ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama ƴan ƙasashen waje da dama da ake zarginsu da ɗaukar nauyin zanga-zangar da ake gudanarwa a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar,Salman Dogo shi ne ya bayyana haka ranar Talata bayan ganawar da ya yi da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.

Masu zanga-zanga a jihar sun fara ɗaga tutar Rasha a ranar farko ta zanga-zangar inda suke kira ga shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin da ya kawo ɗauki.

Yayin ɗaga tutar ya watsu ya zuwa biranen Jos, Abuja da Kaduna  inda masu zanga-zanga suka fantsama kan titi ɗauke da tutar ta Rasha.

Dogo ya ce hakan ya kawo damuwa a tsakanin hukumomin tsaro har ta kai ga an kama ƴan ƙasashen wajen bayan da aka zurfafa bincike.

Kwamishinan ƴan sandan ya ce hukumomi na ɗaukan duk matakan da suka dace domin tabbatar da dawo da zaman lafiya da doka-da- oda  ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya rage wa’adin dokar hana fita daga ƙarfe sa’o’i 24 ya zuwa 12.

More from this stream

Recomended