An kai hari wani ƙauye a Bauchi, an yi garkuwa da ɗa da matar basarake

Mutum daya ya rasa ransa yayin da daya ya jikkata sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai ranar Litinin a kauyen Magamin Kano da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.

‘Yan bindigar sun kuma kai farmaki gidan Hakimin kauyen Alh. Bashir Abubakar, kuma sun yi garkuwa da matarsa da dansa zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun harbe mutum guda har lahira, yayin da kuma aka jikkata wani a cinyarsa amma yana samun kulawa a babban asibitin Ningi.

A cewar majiyar, basaraken ne aka fi kaiwa hari, amma ya samu nasarar tserewa, amma matarsa da dansa ba su yi sa’ar tserewa ba. An yi garkuwa da su.

More from this stream

Recomended