An kai hare-hare kan matatun mai na Saudiyya da jirage BBC Hausa

•Abqaiq matatar mai ce mafi girma a duniya

Kafofin yada labarai na gwamnatin Saudiyya na cewa an kai wasu hare-hare da jiragen sama masu sarrafa kansu a gabashin kasar.

An dai kai hare-haren ne kan wasu wurare biyu da ake sarrafawa da adana albarkatun man fetur.

Jami’an gwamnatin kasar sun ce gobara ta tashi a sanadiyyar hare-haren musamman a matatar mai ta Abqaiq – wanda ita ce irinta mafi girma a duniya – da kuma a Khurais, inda ake hako mai.

Kafofin watsa labarai na Saudiyyar sun ce an shawo kan gobarar da ke ci. Tun farko, hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gobarar ta haska samaniya a Abqaiq.

A wasu bidiyon, ana iya jin karar harbe-harbe a bayan fage, tamkar ana gwabza fada.

Babu wanda ya san takamamai wdanda suka kai wanann harin.

Matatar mai ta Abqaiq na karkashin kulawar kamfanin mai na Saudiyya ne wato Aramco.

Abqaiq na da nisan kilomita 60 a kudu maso yammacin Dhahran a lardin gabashin Saudiyya, inda Khurais kuwa na da nisan kilomita 200 ne kudu da Abqaiq, wanda shi ne wuri na biyu a girma da Saudiyya ke hako man fetur.

Dakarun Saudiyya sun taba dakile wani hari da al Qaeda ta so ta kai a yankin a 2006. Kuma Saudiyya ta rika amfani da makaman ta na kariya wajen dakile wasu hare haren da ‘yan tawayen Houthi ke kai wa daga Yemen.

Wadanda ake ganin su ne suka kai hare-haren

An dora alhakin kai wasu hare-hare da aka kai cikin Saudiyya kan mayaka ‘yan Houthi na kasar Yemen.

A wancan karon, sun kai hari ne kan wata masana’antar samar da iskar gas a Shaybah cikin watan Mayu, har ma da wasu wuraren da ake sarrafa man fetur.

Kungiyar ta ‘yan Houthi na da alaka ta kut-dakut da kasar Iran, kuma tana neman kwace iko ne daga hannun gwamnatin Yemen wadda hadakar kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta ke mara wa baya.

[ad_2]

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...