An hallaka ƴan ta’adda a Borno

Sojoji sun hallaka aƙalla ‘yan ta’addar Daesh 55 daga cikin ‘yan ta’addar ISWAP.

Cikin wadanda aka kashe har da wasu manyan kwamandoji da dama ajihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar ma’aikatar tsaron kasar Nijar, rundunar hadin gwiwa ta Sector 3 da Sector 4 Multinational Joint ne suka shirya wani gagarumin farmaki na kwanaki 22 da aka yi wa lakabi da Operation HARBIN ZUMA, wanda aka fara a ranar 6 ga Mayu, 2023, kuma ya kare a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu.

Wasu daga cikin manyan kwamandojin sun hada da Fiya Abouzeid, Qaïd Abou Oumama da Qaïd Malam Moustapha, da kuma wasu malaman addini da har yanzu ba a san sunayensu ba.

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...

An dakatar da dokar hana fita a Kano

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bayar da sanarwar kawo karshen dokar hana fita ta tsawon sa'a 24, da aka sanya a jihar.Mai...