An gama aikin ceto mutanen da ke ƙarƙashin ginin benen da ya rufta a Lagos

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, LASEMA, Adesina Tiamiyu, ya ce ya zuwa yanzu babu wani mutum da ya rage cikin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguzo a yankin Ita Faji dake jihar.

Tiamiyu ya bayyana haka lokacin da yake magana da yan jaridu a wurin da lamarin yafaru.

“Mun dakatar da aiki da misalin karfe uku na dare bayan da muka zakulo gawar wani mutum, mun tabbata cewa babu wanda yayi saura karkarshin baraguzan ginin,” ya ce.

Amma wasu mazauna yankin sun musalta ikirarin na shugaban hukumar ta LASEMA inda suka dage kan cewa har yanzu akwai sauran mutane da suka rage a karkashin baraguzan ginin.

Ginin benen mai hawa uku dake ɗauke da makarantar firamare a hawa na biyu ya rufta ranar Laraba da safe lokacin da dalibai suke tsaka da karatu cikin ajinsu.

Akalla mutane 12 ciki har da yara tara aka tabbatar da mutuwarsu.

More News

Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...