An ceto ɗaliban jami’ar Zamfara guda 14 da ƴan bindiga suka sace

Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara ta bayar da sanarwar cewa ya zuwa yanzu an ceto ɗalibai 14 da leburori biyu waɗanda ƴan bindiga suka awon-gaba da su a daren Juma’ar da ta gabata.

Cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar, na cewa a jimilla, an kuɓutar da mutum 16, 14 dalibai, 2 kuma ma’aikata tun bayan sace su da aka yi.

Jami’ar ta kara da cewa waɗanda suka shiga firgici a hannun ƴan bindigar, tuni aka haɗa su da iyalansu.

Haka nan sanarwar ta buƙaci ɗalibai da malaman jami’ar su ci gaba da tafiyar da lamurransu kamar yadda suka saba.

Ta kuma yaba wa jami’an tsaron Najeriya bisa ƙoƙarin da suka yi na ƙwato waɗanda aka sace.

More News

Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar...

Masu cin gajiyar shirin Npower na kokawa game da rashin biyansu

Wasu masu cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na N-Power a ranar Litinin sun koka kan yadda ake ci gaba da biyan su alawus-alawus din...

Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL

Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL). An bayyana hakan ne...

Ba baƙon abu ba ne don an haifi yaro da haƙori a bakinsa—in ji masana lafiyar yara

Likitocin kula da lafiyar yara sun ce jariran da ke da hakora daya ko biyu a lokacin haihuwa hakan ba baƙon al'amari ba ne. Wannan...