An ba wa mata 1000 jari a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano

Mai girma Uwargidan gwamnan Jihar Kano, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, da Uwargidan shugaban jam’iyyar APC jihar Kano, Hajiya Zainab Abdullahi Abbas, sun jagoranci taron kaddamar da ba wa mata kimanin dubu daya 1000 jari na kayan sana’a wanda suka hada da keken dinki, injin taliya da fulawa, injin jannareto, da kudi naira dubu Goma ga kowace mace a ranar Asabar.

Haka ma an raba Al-Qur’ani mai tsarki ga makarantun Islamiyoyi tare da Masallatai duk a karamar hukumar Gwale karkashin sahalewar shugaban jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas da Hon. Dakta Khalid Ishak Diso shugaban karamar hukumar Gwale kuma sarkin yakin Ganduje.

A lokacin da shugaban karamar hukumar ta Gwale Hon. Dakta Khalid Ishak Diso yake jawabi, ya nuna farin cikin sa da godiya ga Allah tare da matar gwamna bisa yadda take tallafawa mutane musamman Mata da kananun yara kuma Allah ya azurta jihar Kano da jajirtaccen gwamna mai kishin al’umma sa, ya ce hakika zuwan gwamna alheri ne domin kullum burin sa tallafawa maza da mata da yara marayu da ‘yan makaranta, inda ya ce gwamna Ganduje ya yi abun da ba za a tabs manta da shi ba a Gwale domin ya gina Azuzuwan makaranta, Asibiti, Hanyoyi, Ruwan Sha da sauran su kuma Hon. ya kara tabbatarwa Uwargidan gwamnan Kano cewar al’ummar karamar hukumar Gwale sun ce Ganduje za su yi ba su san kowa ba sai shi dan haka Ganduje ya ci zabe a Gwale ya gama da izinin Allah.

Shima mai girma shugaban Alh. Abdullahi Abbas ya yin nasa jawabin ya nuna farin cikin sa matuka da gaskiya bisa yadda Allah ya nuna wannan ranar farin cikin na tallafawa mata da jari domin su dogara da kan su, ya kara da cewar mu a nan Gwale APC Sak za mu yi tundaga kan shugaban kasa Muhammadu Bubari zuwa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje zuwa Sanata Malam Ibrahim Shekarau tare da dan majalissar tarayyar mu Hon. Lawan Kenken da dan autan su Hon. Usman Rabiu na majalissar jiha wanda dukkan nin su rantsuwa kawai suke jira domin sun ci zabe sun gama da yaddar Allah. Ya kuma kara da cewa a cikin tallafin nan kowanne da sunan sa akwai Gwaggo saboda matan da aka bawa yan halak ne, akwai tallafin Allah ya raya Ganduje bisa nuna godiya da jin dadin mulkin sa cikin shekaran da ya yi yana mulki duk yaron da aka haifa a Gwale to yaro ne mai albarka ta rayuwa, A karshe Alh. Abdullahi Abbas ya ce mu Matan mu dake Gwale masu rukon amana ne kuma dan takarar gwamnan PDP dan Gwale ne kuma wurin zaben su daya da Uwargidana amman ko ita sai ta kayar da shi, sannan nan da bayan zaben shugaban kasa zamu sake bawa mutane dubu daya 1000 tallafi a wannan karamar hukumar ta mu ta Gwale da yaddar Allah.

An gudanar da wannan gagarumin taron ne a cikin sakatariyar karamar hukumar Gwale wanda ya samu halartar wakilin gwamna, hakimin Gwale da Uwargidan mataimakin gwamnan jihar Kano da mataimakin shugaban karamar hukumar ta Gwale tare da ‘yan takarkarun kujeru daban daban daga cikin da wajan kananan hukumomi arba’in da hudu 44 dake Kano, da kuma manyan jami’an gwamnati daga matakin jiha da kansiloli masu bayar da shawara da masu taimakawa shugaban karamar hukumar ta Gwale a fannoni da kuma al’ummar Gari.

Anas Saminu Ja’en Mataimaki Na II, Ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale Akan Sababbin Kafafen Yada Labari.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...