An ɗage sauraron shari’ar Hadizan Gabon

0

Khadi Rilawanu Kyaudai na kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Magajin Gari Zariya,ya dage shari’ar da yake sauraro tsakanin yar wasan Kannywood, Hadiza Gabon da Kuma Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa.

Ana tuhumar Gabon da laifin zanbatar Bala bayan da ta karɓe masa yan kudade da sunan zata aure shi.

An dage zaman shari’ar zuwa ranar, 1 ga watan Agusta biyo bayan yanayin rashin lafiya da matar alkalin take ciki.

Musa ya kai karar ne inda yake bukatar jaruma Gabon ta dawo masa da kudinsa,396,000 bayan da taki amincewa ta aure shi.

Tuni dai jarumar ta musalta cewa akwai wannan alƙawari a yayin zaman kotun da aka yi na farko a ranar 14 ga watan Yuni.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa bayan da kowa ya gama hallara domin fara sauraren shari’ar na ranar Talata sai alkalin ya sanar cewa ya samun labarin an kai ɗaya daga cikin matansa a asibiti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here