Al’ajabi: Wata ta haifi tagwaye wata daya bayan haihuwar jaririnta

Stock photo of a baby's foot

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sultana ba ta san cewa tana dauke da cikin ‘yan uku ba ne

Wata mata ‘yar kasar Bangladesh ta haifi tagwaye bayan kusan wata daya da haihuwar bakwainin danta, kamar yadda likitanta ya shaida wa BBC.

Arifa Sultana, mai shekara 20, ta haifi dan nata ne a karshen watan Fabrairu, amma bayan kwana 26 sai aka sake garzayawa da ita asibiti bayan da ta yi korafin cewa tana fama da ciwon ciki.

Likitoci sun gano cewa tana dauke da cikin ‘yan biyu a mahaifarta, sai suka yi mata aikin gaggawa don cire su.

An ciro ‘yan biyun nata cikin kashin lafiya, kuma daga bisani aka sallame ta daga asibiti ba tare da wata matsala ba.

Mun kadu

Sultana, wacce ta fito daga wani kauye, ta haifi jariri na farkon ne a asibitin koyarwa na Khulna da ke gundumar Khulna.

Bayan kwana 26, sai ta yi korafin ciwon ciki aka sake mayar da ita asibitin Ad-din da ke yankin Jessore ranar 21 ga watan Maris, kamar yadda likitar mata Dr Sheila Poddar, wanda ita ta yi aikin fid da jariran ta shaida wa BBC.

Sai dai wasu kafofin yada labaran sun ce ranar 22 ga watan Maris aka yi aikin.

“A yayin da mara lafiyar ta zo sai muka yi mata hoton ciki inda muka gano jarirai biyu a cikinta,” in ji Dr Poddar.

“Mun kadu matuka kuma mun yi mamaki. Ban taba cin karo da wani abu makamancin haka ba a rayuwata.”

Sai dai ba a san dalilin da ya sa matar ta je wani asibitin daban da wanda ta haihu tun farko ba.

A cewar Dr Poddar, Sultana da mijinta “talakawa ne” kuma ba a taba yi mata hoton ciki ba,” kafin ta haifi jaririnta na farkon.

“Ba ta san cewa akwai wasu jariran a cikinta,’ in ji Dr Poddar. “Sai muka yi mata fida muka ciro mata ‘yan biyu, mace da namji.”

An sallami Sultana da jariranta daga asibiti ranar 25 ga watan Maris, bayan da suka shafe kwana hudu.

“Ita da jariran na cikin koashin lafiya. Ina matukar farin cikin ganin komai ya tafi daidai,” in ji Dr Podda.

Wani likitan mata a Singapore ya ce matar na da mahaifa biyu ne – kuma al’amari ne da ba a faye samu ba a tsakanin mata.

“Idan aka yi hoton ciki da wuri, za a iya gano cewa akwai mahaifa biyu. Sai dai kuma a gaskiya ita wannan mata daga kauye futuk ta fito don haka ba su da hanyoyin yin hoton ciki,” kamar yadda Dr Christopher Ng na asibitin GynaeMD ya shaida wa BBC.

“Ga alama kwayaye uku ne suka shiga mahaifarta a lokaci guda, wanda hakan ne ya sa ta dauki cikin ‘yan uku.”

Ms Sultana ta ce ta yi matukar farin cikin haihuwar ‘yan ukunta amma tana fargabar shiga matsala wajen kula da su saboda halin talauci da take ciki, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Abun da mijinta ke samu a wata bai kai dala 95 ba, (naira 34,200) a matsayinsa na lebura, amma ya shaida wa AFP cewa zai yi iya bakin kokarinsa.

“Wannan wata mu’ujiza ce daga Allah kasancewar ‘ya’yana cikin koshin lafiya. Zan yi bakin kokarina na ga sun kasance cikin farin ciki.”

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...