Akwai Gumurzu a zaben gwamnonin Najeriya

elrufai da kudan

A yau Asabar ne ‘yan Najeriya ke fita don zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki, makonni biyu bayan da aka yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilan tarayya.

Za a yi zaben gwamnonin ne a jihohi 29 daga cikin 36 na kasar.

Zaben gwamnonin dai zai kasance mai cike da gasa saboda irin tataburzar siyasa da ke tattare da su da kuma yadda ake kashe makudan kudade.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP a zaben da aka yi ranar 23 ga watan fabrairu, inda ya samu nasarar zarcewa a karo na biyu.

Jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’a miliyan 15.2 yayin da PDP ta samu kuri’a miliyan 11.3.

APC ta lashe jihohi 19, yayin da PDP ta samu jihohi 16 da kuma babban birnin kasar, Abuja.

Akwai jihohi bakwai da ba za su yi zaben gwamna ba saboda gwamnoninsu ba su kammala wa’adinsu ba.

Duk da cewa mutane ba su yi tururuwar fita zaben ba a duk fadin kasar, yawan wadanda suka fita zaben sun fi daga arewacinta – wanda hakan na daga cikin dalilan da suka taimakwa Buhari wajeb samun nasara.


Zaben shugaban kasa cikin alkalumma

  • Masu katin zabe mutum miliyan 84
  • Yawan wadanda suka fita zaben kashi 36 ne cikin 100
  • Buhari ya samu kuri’a miliyan 14
  • Atiku ya samu kuri’a miliyan 11

Sharhi Daga Aliyu Tanko

Alal misali, an yi kiyasin cewa jihar Legas na da yawan mutane miliyan 17.5; wannan ya fi yawan al’ummar kasashen Gabon da Gambiya da Laberiya da Cape Verde ds kuma Saliyo idan aka hada.

Kuma tattalin arzikinta ya fi na Kenya. A takaice dai, da a ce Legas kasa ce mai zaman kanta, to tabbas da za ta zamo ita ce ta biyar ma fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Gwamnoni a matsayinsu na masu mulkin jihohin suna iya sanya doka idan majalisar dokoki sun amince musu ne kawai.

Misali, a shekara ta 2000 – Gwamnan Zamfara Ahmed Sani Yerima ya kaddamar da Shari’ar Musulunci a jiharsa har ma wasu gwamnonin arewacin kasar suka bi sahunsa, duk da cewa gwamnatin tarayya ba ta karbi lamarin sosai ba.

An kama wasu gwamnonin kasar da laifin halatta kudin haram da zamba kamar James Ibori, wani tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur a kudancin kasar, kuma an daure shi tsawon shekara 13 a gidan yari a Birtaniya kan zambar kimanin dala miliyan 50.

Ko da gwamnatin tarayya kanta, tana bukatar goyon bayan gwamnonin jihohi kafin daukar wasu manyan matakai da suka shafi kasa, kamar yadda suka kalubalanci aniyar gwamnatin tarayya a kotuna don cire dala biliyan daya daga asusun danyen man fetur na kasar domin kaddamar da asusun zuba jari.

Duk da cewa ana ganin zaben wannan Asabar din a matsayin mai zafi tsakanin manyan jam’iyyun kasar biyu – APC da PDP, amma akwai jihohin da a nan ne za a fi fafatawa.


A yayin zaben shugaban kasar, kowace jam’iyya na zargin dayar da hada kai da INEC don yin magudi a zaben, wanda tun farko aka sanya za a yi shi ranar 16 ga watan Fabrairu, amma sai aka daga shi zuwa 23 ga wata, sa’o’i kadan kafin a bude rumfunan zabe.

Mista Buhari ya yi alkawarin karasa ayyukan da ya fara a karonsa na farko, yayin da Atiku Abubakar fitaccen dan kasuwa, ya zarge Buharin da bata shekaru hudunsa na farko “a banza”.

Sai dai tun farko masu sharhi sun yi hasashen cewa duk wanda ya yi nasara zai fuskanci kalubale da dama.


Gumurzun da za a yi a zaben gwamna

A yanzu haka abin da ‘yan kasar suka zura ido su gani shi ne irin gumuruzun da za a yi a zaben na gwamna a ranar Asabar.

Akwai jihohi kalilan da tuni aka yi hasashen ‘yan takarar da za su lashe zaben jihohin sakamakon karancin karfin jam’iyyun adawa.

A wasu jihohin kuma, kamar mace ce mai ciki, ba a san abin da za ta haifa ba, saboda girman adawa tsakanin ‘yan takara a jihohin inda da wuya a iya hasashen wanda zai iya lashe zaben gwamna a jihohin.

Jihohin da ake ganin zaben gwamna zai fi zafi sun hada da Kano da Sokoto da Kaduna da Gombe da Lagos da Akwa Ibom da Imo.

Sharhi, Mustapha Kaita

Kamar yadda ake yi wa kallon siyasar Kano sai dan Kano kuma ‘Kano ta dabo tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika,’ hakan ya sa ake ganin zaben gwamna a 2019 a Kano zai fi zafi fiye da sauran jihohin.

Za a fafata ne tsakanin gwamna mai ci da ke neman tazarce Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da kuma dan takarar Kwankwasiyya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP.

Ana ganin zaben gwamna Kano, fafatawa ce tsakanin tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa gwamna Ganduje wadanda suka yi shekara takwas a gwamnati.

A Kaduna kuwa ana ganin zaben gwamna zai ja hankali musamman tsakanin ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasa wato APC da kuma PDP.

Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai dan takarar APC zai fafata ne da babban mai hamayya da shi Isah Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP, kuma a yanzu haka masu sharhi na cewa tui siyasar jihar ta dauki bangaranci na addini da kabilanci.

Gombe na daga cikin jihohin da ake ganin za su ja hankali a zaben gwamna.

Jam’iyyar APC mai adawa za ta yi kokarin kwace mulki ne daga hannun jam’iyyar PDP da ke mulka a jihar.

Za a fafata ne tsakanin Usman Bayero Nafada na jam’iyyar PDP da kuma dan takarar jam’iyyar APC Inuwa Yahaya, wacce ake gani tamkar tsakanin gwamna mai barin gado ne Hassan Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Danjuma Goje.

A Sokoto kuwa, Gwamna Tambuwal ne ke neman tazarce a wa’adi na biyu inda zai yi takara tare da tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu wanda APC ta tsayar dan takararta kuma wanda tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko ke marawa baya.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...