Akwai Bukatar A Yi Nazari Sosai Kafin A Dauki Jami’in Tsaro Aiki | VOA Hausa

Sufeto Janar na ‘yansandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ce an ceto ‘yan Najeriya 837 wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su sannan an samu nasarar kwato makamai 1,356 a hare haren da jami’an tsaro suka kai a fadin kasar. Hakazalika an kama harsasai dubu 21,300.

Kwararre a harkar tsaro na kasa da kasa kuma shugaban kamfanin tsaro na BICON Securities, Kabir Adamu, ya ce abinda ya kamata shi ne a yi kokarin gurfanar da masu laifi a gaban kotu saboda a hukunta su akan laifukan da suka aikata, domin yin haka zai yi nuni ga wadanda ke da niyar shiga wanan hali na ta’addanci cewa ba aiki ne mai kyau ba, saboda haka za su ji tsoron yi, abu na biyu kuma a ja su kusa da jiki domin a yi kokarin sauya masu dabi’a domin an lura yawancin su ba su da ilimin addini ko na boko, saboda haka nuna masu kula yana iya sauya tunanin su.

Ganin yadda kwararru ke bayanin cewa akwai alaka tsakanin ta’addanci da batun sauya dabi’a, Farfesa Otaki Osana Alananan, na Jami’ar Abuja ya ce a rika bin diddigin irin mutanen da za a dauka a aikin jami’in tsaron kasa, ba kawai a debi kowane irin mutane ba. Ya bada shawara akan a koma salon daukar aiki da ake yi a baya, inda ake sanin asalin mutum kafin a dauke shi aikin jami’in tsaro, ya ce yin haka zai rage cin hanci da rashawa da ya yi katutu a jami’an tsaron kasar.

Shi ma Tsohon Shugaban Hukumar Wayar da kan al’umma ta kasa wato NOA, dakta Mike Omeri, ya ce akwai rashin shugabanci ingantacce saboda haka dole ne a wahala kafin a ja hankalin mutane su rika hadin kai wajen mu’amalar da zata kawo zamantakewa mai ma’ana saboda a rinka fahimtar juna koda a wajen musayar ra’ayi ne.

Dakta Omeri yace da shi da wasu ‘yan’uwansa suna kokarin fito da tsarin da zai taimakawa shugabanni da al’umma baki daya wajen gyara dabi’unsu.

Ya kuma yi fatan yin hakan zai taimaka wajen kawar da kyama da rashin jituwa a tsakanin al’umma.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...