Akpabio da Abbas na ganawa da ƴan ƙungiyar ƙwadago

Mambobin gamayyar kungiyoyin ƙwadago na can na wata ganawa da shugaban majalisar dattawa sanata Godswill Akpabio da kuma shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Tajuddeen Abbas.

Ganawar na gudana ne biyo bayan shirya tsunduma yajin aiki da kungiyar ƙwadago ta shirya shiga a ranar 3 ga watan Yuni.

Joe Ajaero shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC da takwaransa na ƙungiyar TUC, Femi Osifo sune suka jagoranci sauran shugabannin kungiyar ya zuwa wurin taron.

Godswill Akpabio da Tajuddeen Abbas sun kira taron ganawar ne a ƙoƙarin da suke na ganin an cimma matsaya a tsakanin gwamnati da ƴan kungiyar ƙwadagon kan maganar mafi girma ƙarancin albashi.

A ranar Juma’a ne NLC da TUC suka ayyana tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani bayan da gwamnatin tarayya ta ƙi ƙara mafi ƙarancin ƙarancin albashi daga ₦60,000

A ƴan kwanakin baya ne ɓangaren gwamnati, ƙungiyar ƙwadago dana masana’antu masu zaman kansu suka fara tattaunawa kan batun ƙarin mafi ƙarancin albashi.

Tun da farko kungiyar ƙwadago ta nemi a biya ₦615,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi duba da yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamnatin tarayya tayi watsi da buƙatar inda ta ce za ta biya ₦48,000 bayan ƙin amincewa da ƙungiyar ƙwadagon gwamnatin tarayya ta sake ƙara kuɗin ya zuwa ₦60,000 inda suma masu masana’antu suka amince da sabon ƙarin.

More from this stream

Recomended