AFCON: ‘Yan Algeria 5,000 sun daga wa Masar hankali

Algerian fan shows the Egyptian flag during the semi-final match against Nigeria

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shin ‘yan Aljeriya da Masar sun warware rashin jituwar da ke tsakaninsu a fagen kwallon kafa?

—BBC Hausa

Labarin cewa mutum 5,000 ne suka tafi Masar daga Aljeriya don goyon bayan kungiyar kwallon kafar kasarsu a wasan da za ta yi ranar Juma’a ya daga hankalin hukumomin Masar din wata kila ma har da hana su barci.

Kasashen biyu manyan abokan adawar juna ne a tarihin kwallon kafa na duniya, kuma an sha samun tashin hankali a fafatawar da ake tsakanin kungiyoyin kasashen biyu a cikin filin wasa ko a wajensa.

Sai dai a wannan karon abubuwa sun sha bambam:

Na farko, tuni aka fitar da kungiyar kwallon kafa ta Masar a gasar cin kofin Afirkar da ake a kasar a zagaye na 16 bayan da Afirka Ta Kudu ta fitar da su a wani lamari da ya zo wa mutane da mamaki.

Fitar da su din ya zama silar kaucewa duk wani tashin hankali da aka yi tunanin zai iya faruwa tsakaninsu da makwabciyar tasu Aljeriya.

Iface-iface

Na biyu, kuma abu mafi ban mamaki: al’ummar kasar sun yi maraba da ‘yan Aljeriyan wadanda ake kira da Kuregun Hamada.

A yayin da Aljeriya ta yi nasara a kan Najeriya 2-1 a wasan kusa da karshe a ranar Litinin, an ga yadda ‘yan Masar da dama suka dinga murnar nasarar makwabciyarsu – kuma ga alama haka za su yi a ranar Juma’a ma a wasan da za ta buga da Senegal.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tempers have flared up before, during and after past encounters between Egypt and Algeria

A takaice dai dukkan magoya bayan kasashen biyu Aljeriya da Masar sun hada kai wajen bujirewa hukumomin Masar a yayin wasan daf da na karshe inda suka dinga ihu tare da kiran sunan wani tsohon dan wasan Masar Mohamed Aboutrika, wanda yake neman mafaka a wata kasar bayan da ya soki mulkin soji karara.

Bayan da aka gama wasan, dan wasan gaba na Aljeriya Youcef Belaili ya ce “Godiya ga ‘yan Masar da suka goya mana baya, Allah ya ji kan shahidanmu.”

Ba wanda ya taba tunanin irin haka za ta faru. Ko da kuwa an sa batun yanayi da zamantakewa a nahiyar Afirka – inda Masar da Aljeriya ‘yan Afirka ta Arewa ne kuma Larabawa, ba kamar sauran kasashen nahiyar 52 ba.

Rigimar da ta wuce

A tarihi, akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu – Masar ta mara wa Aljeriya baya lokacin da take yakin neman ‘yancin kanta daga kasar Faransa a shekarun 1954 zuwa 1962.

Sai dai wasannin kwallon kafa kan kare da rikici tsakaninsu a lokuta da dama.

Mafi shahara daga ciki shi ne wanda ya faru a shekarar 1989 a wasan neman cancantar zuwa Kofin Duniya, wanda har ake masa lakabi da “Yakin Alkahira” (Battle of Cairo).

Nasarar da Masar da ta yi a wasan ya ba ta damar halartar gasar cin Kofin Duniya na shekarar 1990. Rikicin da ya biyo bayan wasan ya yi sanadiyar makantar da wani jami’in tawagar kwallon kafar Masar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tauraron dan wasan Aljeriya Belloumi (daga dama) ya fusaknaci shari’a ta tsawon lokaci kan “Yakin Alkahira”

Mahukuntan Masar sun zargi Lakhdar Ballouni saboda rikicin, inda aka dauki shekara 20 ana neman kama shi bisa umarnin kotu a kasar.

A shekarar 2009 ma kassashen sun gwabza da juna a wasan cancantar shiga Kofin Duniya. Bayan kowacce ta ci wasan gidanta da 2-0 sai aka ci gaba da buga wasan a birnin Khartoum na Sudan.

An buga wasan ne yayin da shugaban kasar Masar Hosni Mobarak ya yi barazanar tura sojoji domin tsaron lafiyar magoya bayan tawagar kasarsa.

An yi ta zanga-zanga a kasashen biyu, abin da ya kai ga lalata shagunan kasuwancin Masar a kasar Aljeriya.

Aljeriya ce ta lashe wasan da ci 1-0.

Watanni bayan haka, a shekarar 2010 an sallami ‘yan wasan Aljeriya uku daga wasan cin Kofin Afirka tsakanin kasashen.

Yayin magoya suka rika fadar maganganu kan Aboutrika a kafafen sada zumnta, ita kuwa hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF tana bincike ne kan karawa tsakanin magoya bayan Aljeriya da Masar a wasan kusa da na karshe da Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Aljeriya sujn yi ta murna har a titun birnin Paris na Faransa

Mahukuntan Masar sun tsaurara tsaro yayin gudanar da gasar musamman kusa da filayen wasanni. Wani mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida ya ce har yanzu ba a samu rahoton rikici ba.

Ya ce: “‘Yan Aljeriya sun yi murnar nasarar da suka samu tare da ‘yan kasar Masar ba tare da wani rikici ba.”

Wani hoto da wata jaridar Masar Al Ahram ta wallafa a shafinta na Intanet ya nuna wani dan Aljeriya da dan Masar suna murna tare da kuma nuna ‘yan uwantaka.

Wani dan Masar Mohammed Mosen ya ce: “Mun yi abota da su kuma mun koyi wakokinsu har ma muka rika rera shahararren takensu na ‘1, 2, 3 vive l’Algérie,’ kuma sun ji dadin yadda muka goyi bayansu.

Mun yi imamnin cewa sun cancanci mu goyi bayansu saboda su ne kan gaba zuwa yanzu a filin kwallo da kuma kokarinsu.”

Sai dai abu ne a boye ko wannan ‘yan uwantakar za ta dore har zuwa karshen wasan.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...