A hana Fulani tafiya da Shanu zuwa Kudu – Ganduje | BBC Hausa

Fulani makiyaya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani kwamiti wanda zai fito da tsarin yadda za’a fara aiwatar da shirin samar da rugagen Fulani na zamani.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa BBC cewa shirin samar da rugar a Kano ba iya Fulanin da ke jihar kawai ne za su amfana ba har da na sauran jahohin Najeriya.

Ya kuma ce shirin shi ne kawai da zai kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Wannan na zuwa a yayin da ake ci gaba da musayar kalamai game da kiran Fulani su baro kudancin Najeriya da suke tafiya kiwo zuwa yankin arewaci.

Gwamna Ganduje ya ce dole a canza yadda ake gudanar da tsarin kiyo idan ana son magance matsalar rikicin makiyaya da manoma.

“Idan dai har ana son rigimar nan a daina ta dole a hana fulani tafiya da shanu daga arewa zuwa kudu,” in ji shi.

Ya kuma ce dole ya kasance a arewa an yi wuraren kiyo ga duk wanda zai yi kiyon shanu.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Gwamnan ya ce shirin ruga a Kano ya kunshi samar wa fulani hanyoyi na zamani ta hanyar ba ‘ya’yansu ilimi da asibiti da kuma banki na Islama da samar da kiyo na zamani da kuma yadda shanu za su samu abinci domin samar da wadataccen nono.

Gwamnatin Kano dai ta dage kan kaddamar da shirin duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da kudirinta na samar da rugagen, saboda yadda kudirin ya janyo ce-ce-ku-ce.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...