A Gobe Juma’a Ne Shugaba Buhari Zai Shilla Zuwa Kasar Chana

[ad_1]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a gobe Jumma’a zai kai ziyarar aiki kasar Sin (China) Domin halartar Babban taron hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afurka (FOCCAC) wanda za a gudanar karo na 7 a Beijing Babban Birnin kasar ta China, a Ranar Litinin 3 watan Satumbar shekara ta 2018.

Shirin farko na shugaban kasar a Beijing zai yi ganawa ne ta musamman tare da kungiyar ‘Yan Asalin Najeriya mazauna kasar Sin a ofishin jakadancin Najeriya a kasar China. Kafin a bude taron kolin na FOCAC.

A yanzun Shugaba Buhari shine Shugaban kungiyar ECOWAS na yanzu, ana sa ran zai gabatar da jawabinsa a babban taron na tattaunawa da za’ayi tsakanin shugabannin Sin da Afrika, wanda ya kumshi wakilan kasuwanci da kuma ‘yan kasuwa na Afrika.

Shugaban kasar Nijeriya zai shirya ziyararsa tare da shugaban kasar Jinping da wasu shugabannin Afrika don bude taron da aka yi a taron dandalin tattaunawa na Beijing karo na 2018 a karkashin batun: “Zuwa gagarumin karfi na kungiyar Sin da Afirka da ke da nasaba da gaba.”

Bayan kammala taron na FOCAC, shugaban kasa Buhari zai yi ganawa ta Musamman da Shugaban kasar Sin (China) Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang don tattauna hanyoyin samar da albarkatun kasa a kan ayyukan da aka yi a Najeriya da kuma inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya. Domin duba tare da nazarin nasarar da aka samu a yanzu a cikin ayyukan da Sin ke yi da ayyukan samar da agaji a Nijeriya, musamman ayyukan ci gaban da ke cikin tashar jiragen kasa da na wutar lantarki.

Shugaba Buhari zai ziyarci Beijing tare da rakiyar Uwargidansa Aisha Buhari, wanda ke shirin shiga cikin shirin Matan Sin da Afrika na hadin gwiwa game da cutar AIDS.

A yayin Ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu Rakiyar Gwamnonin da suka hada da na jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar, da gwamnan jihar Lagos Akinwunmi Ambode, da na jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar, da gwamnan jihar Imo Rochas Anayo Okorocha.

Sauran sun hada da Sanata Abdullahi Adamu, daga jihar Nassarawa, George Akume daga jihar Benue, sai Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom, da kuma Sanata Aliyu Wamakko daga jihar Sokoto.

Har ila yau, a tare da shugaban kasar a yayin Tafiyar akwai Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Ministan Birnin Tarayya Abuja Mal. Muhammad Bello da kuma Ministan Harkokin Kasuwanci, Ciniki da Zuba Jarurruka, Okechukwu Enelamah; Ministan kasafi da tsare-tsare Udoma Udo Udoma; Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu; Ministan Harkokin Man fetur, Ibe Kachikwu, da Ministan Sufurin jiragen sama Sen. Hadi Abubakar Sirika.

Sauran tawagar sune mai bada Shawara na Musamman kan sha’anin Tsaro na kasa, Babagana Monguno; Babban Darakta, Hukumar Tsaro ta Duniya, Ahmed Abubakar; da kuma Manajan Daraktan Kungiyar, NNPC Maikanti Baru.

Muna masa fatan alheri, da fatan za a tafi lafiya a kuma dawo gida Nijeriya lafiya. Allah ya bada nasarar tafiya. Amin.

[ad_2]

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar ƙera bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...