Ćłanfashi da makami sun Akashe mutane 12 a wani hari kan wasu bankuna biyu a jihar Edo

[ad_1]








Mutane 12 ake fargabar sun mutu lokacin da wasu yan fashi da makami suka kai hari ofishin ƴansanda da kuma wasu bankunan kasuwanci biyu a jiya Talata dake Igarra, hedkwatar ƙaramar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo.

Bankunan da abin ya shafa sune Bankin Unity da kuma Keystone.

Cikin mutane 12 da aka kashe a harin akwai É—ansanda, É—aurarru biyu da kuma wasu kwastomomin bankin.

An gano cewa yan fashin sai da suka fara kai hari ofishin Ć´ansanda dake kusa da bankin a wani abu da ake gani sun yi ne domin hana Ć´ansandan mayar da martani yayin da suke aikata fashin.

Ƴanfashin sun kuma kona sabuwar motar aiki ta sabon baturen ƴansanda na shiya da aka tura yankin suka kuma kashe d’ansanda daya da kuma wasu dake daure a ofishin.

ĆŠaurarru an an kama sune da safe kan rashin cikakkun takardun abin hawa.

An gano cewa yan fashin sun gaza samun nasarar shiga ma’ajiyar kudin bankunan inda suka shiga harbin mutanen dake harabar.

Mai magana da yawun rundunar Ć´ansandan jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin.




[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...