Ƙungiyar CAN ta taya Buhari murnar cin zabe

Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN reshen jihohi 19 na arewacin Najeriya ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar nasara cin zaben shugaban kasa da aka gudanar makon da ya gabata.

An dai zabi Buhari a zaben kasar da aka gudanar ranar 23 ga watan Faburairu inda ya kayar da babban abokin adawar sa na jam’iyar PDP, Atiku Abubakar wanda tuni ya yi watsi da sakamakon zaben.

A wata wasika da kungiyar ta aikewa shugaban kasa mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Faburairu, kungiyar ta CAN reshen arewacin Najeriya,ta ce nasarar da Buhari ya samu wata sheda ce dake nuna gaskiyarsa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga shugaban kasar da ya kafa gwamnatin da za ta hada mutane daga kabilu daban-daban dake kasarnan.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...