Ɗan Boko Haram Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji

Wani mamba a ƙungiyar ƴan ta’adda ta Boko Haram ma suna, Sajeh Yaga ya miƙa kansa ga dakarun rundunar Operation Haɗin Kai dake arewa maso gabashin jihar Borno.

Bayanai sun bayyana cewa ɗan ta’addar ya tsere ne daga sansanin mayaƙan  kungiyar ta Boko Haram dake Yale a dajin Sambisa inda ya miƙa kansa ga dakarun 112 Task Force Battalion dake Mafa a ranar 28 ga watan Afrilu.

Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa ɗan ta’addar ya mikawa sojoji bindiga ɗaya ƙirar AK-47, gidan zuba harshin bindigar Ak-47 guda huɗu, harsashi guda shida sai kuma wayoyi ƙirar Tecno guda uku.

More from this stream

Recomended