Ɗaliban Kuriga: Ko sisi baza mu biya kuɗin fansa ba a cewar gwamnatin tarayya

Shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin cewa kada a biya masu garkuwa da mutane ko sisi duk kuwa da matsin lambar da za ayi.

Ministan sadarwa da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris shi ne ya bayyana haka bayan an kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Ministan ya ce gwamnati na aiki babu dare babu rana wajen ganin cewa waɗanda aka yi garkuwa da su sun dawo gida wajen iyalansu.

A jihar Kaduna ɗaliban da basu gaza 200 ne ba  da malamansu aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuriga da kuma wasu mutane 16 da aka ayi garkuwa da su a ƙauyen Gonin Gora kuma dukkansu na hannun masu garkuwa da mutane.

A jihar Sokoto ma mutane 15 aka sace daga ƙauyen gidan Bakuso a yayin da aka rawaito ƴan ta’addar Boko Haram sun yi garkuwa da mata 50 a jihar Borno.

Da yake amsa tambayoyin ƴan jaridu a fadar shugaban ƙasa, ministan ya yadda an samu ƙaruwar kai hare-hare a ƴan kwanakin nan inda ya ce gwamnati na sanya idanu sosai kan batun a yayin da jami’an tsaro ke cigaba da ƙokarin hana faruwar harin.

Idris ya ce “A yanzu gaskiya ne wasu daga ciki na cigaba da faruwa.Mun ga abun da ya faru a Kaduna, Borno sai kuma Sokoto tabbas gwamnatin’ na sanya idanu sosai ba kawai sanya idanu ba  tana kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna ɗaukar matakan hana haka faruwa sosai.”

More from this stream

Recomended