Ɗalibai 9 aka tabbatar da yin garkuwa da su daga jami’an jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa ɗalibai 9 aka tabbatar sun ɓace bayan da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Confluence dake Osara a jihar.

Ƴan bindigar sun farma jami’ar da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da wasu ɗalibai da ke karatun jarrabawa.

Kingsley Fanwo, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi ya faɗawa manema labarai ranar Juma’a cewa gwamnatin jihar ta tura da jami’an tsaro da kuma ɗaruruwan ƴan bijilante ya zuwa dazukan jihar domin farautar masu garkuwar.

Ya ƙara da cewa an kuma tura ƙarin jami’an tsaro ya zuwa jami’ar.

“Ɗaruruwan mafarauta wanda suka san yanayin  dazukan yankin da kuma sauran jami’an tsaro yanzu haka suna  bincike a yankin domin tabbatar da an ceto ɗaliban  da aka yi garkuwa lafiya daga ajujuwansu,” a cewar Fanwo.

“Kawo yanzu ɗalibai 9 aka tabbatar da rahoton sun ɓace  muna fatan ceto su nan ba da jimawa.”

More from this stream

Recomended