Rundunar yan sandan jihar Taraba ta ce jami’anta sun kama wani mai suna, Aliyu Muhammad akan titin Jalingo-Yola da ake zargin mai garkuwa da mutane.
Joseph Eribo, kwamishinan ƴan sandan jihar shi ne ya bayyana haka ranar Laraba a Jalingo.
Eribo ya ƙara da cewa mutumin da ake zargi ɗan shekara 35 ya fito ne daga karamar hukumar Mubi ƴan sandan kwantar da tarzoma ne suka kama shi a ranar Talata a cikin wata mota ƙirar Toyota mai ɗauke da rijistar namba YLA 321 ZY.
Ya ce jumullar miliyan 8.5 na tsabar kuɗi aka samu a cikin motar sai kuma miliyan 4 a asusunsa na banki, wayoyin hannu guda 7 da katin MTN na 3000 da guraye guda bakwai na daga cikin abubuwan da aka gano a tare da shi.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya yi yinkurin bawa jami’an ƴan sanda cin hanci kafin a kama shi.