Ƴan sandan jihar Bauchi sun kama mutum 9 da ake zargi da fashi da makami

‘Yan sanda a jihar Bauchi sun yi nasarar cafke wasu mutane tara da ake zargi da aikata laifin fashi da makami da addabar mazauna jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Laraba a Bauchi.

Ya kara da cewa, an samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne ta hanyar bajintar kokarin hadin gwiwa na Operation Restore Peace, ORP, da Rapid Response Squad, RRS, na rundunar.

Wakili ya ce, “Game fa aikin sahihan bayanan sirri game da ayyukan kungiyar ‘yan fashi da makami a yankin jami’an suka dauki matakin gaggawa.

“Kungiyoyin sun kasance a karkashin jerin sunayen da ƴan sanda suke son kamawa saboda hannu a fashi da makami.

“A ranar 13 ga Agusta, 2023, da misalin karfe 15:03, ORP ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da suka addabi yankin Bauchi.”

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi ya umurci mutanensa da su ci gaba da gudanar da bincike kan irin wadannan miyagun ayyuka a jihar.

More News

Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar...

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...

An kama ƴan kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan ƴan sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan ƴan...

Masu cin gajiyar shirin Npower na kokawa game da rashin biyansu

Wasu masu cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na N-Power a ranar Litinin sun koka kan yadda ake ci gaba da biyan su alawus-alawus din...