Ƴan sanda sun yi ruwan barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a Abuja

Jami’an ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa akan masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja a yayin da zanga-zanga kan matsanancin halin rayuwa ta shiga rana ta uku.

Masu zanga-zangar sun tattaru a wajen filin wasan inda suke tattauna kan yadda zanga-zangar ranar zata gudana kawai sai hayaƙin barkonon tsohuwa ya fara ta shi.

Ƴan sanda na ƙoƙarin killace masu zanga-zangar a iya cikin filin wasan kamar yadda kotu ta bada umarni tun lokacin da aka fara gudanar da zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta.

“Mu ƴan ƙwallo ne? me yasa za killace a cikin filin wasa,” a cewar ɗaya daga cikin masu zanga-zangar.

A can jihar Lagos jami’an ƴan sanda sun samu nasarar killace masu zanga-zangar a cikin filin Gani Fahenmi Freedom Park.

More from this stream

Recomended