Ƴan sanda sun kama waɗanda suka kashe direba a Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, a ranar Alhamis, ta gurfanar da wasu dalibai uku na wata jami’a mai zaman kanta a jihar Nasarawa bisa laifin kashe wani direban Bolt.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Haruna Garba, ya gabatar da wadanda ake zargin, Obasieyene Inem, Aaron Anthony da Alasan Olusegun, a gaban ‘yan jarida a Abuja.

Garba ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin ya ba da umarnin hawa kan Bolt App don kai su inda suka sayi hodar Iblis

Ya ce a lokacin da aka mayar da su inda suka sayi tikitin tafiya, sai suka gano cewa ba su da kudi a jikinsu, inda ya ce sun yanke shawarar yaudarar direban ne ta hanyar nuna masa sanarwar cire kudi ta bogi a wayar su.

Ya ce, “A ranar 5 ga Yuni, 2023, da misalin karfe 8:30 na dare, an gano wani Obasi Okeke kwance a cikin jini tare da tsaga makogwarosa a Ngugu Close Area 11 Garki, Abuja.

To daga baya ne sai suka fara hatsaniya saboda ya ce musu bai ga kudin da suka tura masa ba. Hakan har ya kai ga kashe shi.

More from this stream

Recomended