Ƴan sanda sun gano masana’antar ƙera a Benue

Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta ce jami’anta sun gano wasu wurare biyu da ake ƙera bindigoga a karamar hukumar Kwande da kuma Guma dake jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito kwamshinan ƴan sandan jihar, Steve Yabanet na cewa an kuma kama wasu mutane uku a maƙerun.

Yabanet ya ce jami’an sun samu bayanan sirri kan masana’antar ƙera makamai a Mbaafa, Adikpo dake karamar hukumar Kwande inda aka kama wani mai suna Friday Aduduakamve da  Iorwashima Iornyume wanda aka fi sani da AK-35.

“ƴan sanda sun bincike masana’antar inda suka gano ƙananan bindigogi guda 9, bindiga ƙirar AK-47 da ba a kammala ba, injin goge ƙarfe guda ɗaya wasu injina guda hudu da kuma sauran kayayyaki iri-iri na ƙera bindiga”

“Tawagar sun kuma gano ƙarin wata masana’antar ƙera bindiga a Daudu dake ƙaramar hukumar Guma inda nan ma aka gano ƙarin wasu makaman.

More from this stream

Recomended