[ad_1]
Lamarin ya faru ne a yau Laraba da misalin karfe uku da rabi a sabuwar Unguwar Railway inda ‘yan daban suka addabi mutanen jihar Kano da fashi da makami.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Majia ya ce jami’an nasu sun yi arrangama da dan daban kuma aka yi nasarar bindige shi bayan sun sassari dan sanda daya a kai, hannu da sassan jikinsa, wanda yake sanye da riga ‘yar shara a jikin sa.
SP MAJIA ya kara da cewa wasu daga cikin wadannan ‘yan daba ko ‘yan fashi da makami da suka gudu sun bar mugayen makaman da suke amfani da su wajen aikata miyagun laifuka bayan arangama da ‘yan sandan kuma jikin gawar dan fashin an sami katin zabe (Voters Card) guda 2 da sunaye daban-daban.
Daga karshe ya bayanna cewa Kwamishinan ‘Yan sanda CP Rabiu Yusuf ya yi jinjina ga DPO na shiyyar Nassarawa CSP Abubakar Argungu da jami’ansa kan samun wannan nasara.
[ad_2]