Ƴan Boko Haram sun yi  garkuwa da matafiya akan hanyar Kano-Maiduguri

Wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun sace matafiya da dama akan hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Wasu majiyoyi sun faɗawa jaridar Daily Trust cewa mayaƙan sun farma matafiyan ne a tsakanin ƙauyukan Garin Kuturu da Mannanari dake kusa da Auno akan hanyar zuwa Damaturu da misalin ƙarfe 05:50 na ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa sun tare babbar hanyar ne kafin suyi amfani da ƙarfi wajen ɗauke wasu fasinjojin.

Matafiya da dama sun yi carkwo-carkwo a dukkanin bangarorin titin biyu dake da yawan motoci masu zirga-zirga.

Wata majiya ta bayyana cewa kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka yi garkuwar da su ba.

More from this stream

Recomended