Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da shugaban jam’iyar PDP na jihar Edo, Tony Anizeigbeme.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da Azeigbeme yan mitoci kaɗan daga kofar gidansa dake rukunin gidajen gwamnati dake Benin babbar birnin jihar Edo.
Masu garkuwa da mutanen sun biyo sawun Azeigbeme a cikin motoci biyu ƙirar Toyota Corolla inda suka wuce motarsa da gudu suka rufe masa hanya kana suka ayi awon gaba da shi ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Shugaban jam’iyar yana kan hanyarsa ne ta dawowa daga gidan gwamnatin jihar bayan kammala wani taron dare kuma baya ta tare da rakiyar ƴan sanda.
Direban Azeigbeme wanda ya yi hira da ƴan jarida ya ce ya lura da wata mata tana bibiyar su lokacin da suka baro gidan gwamnati amma bai yi tunanin cewa masu garkuwa da mutane ne ba.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Edo,SP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar ya umarci rundunar ƴan sanda ta musamman da su bi sawun masu garkuwar kuma su tabbatar da sun kubutar da shugaban jam’iyar.