Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus a mahaɗar Bishini dake kusa da Katari ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Wani mazaunin Katari, Saleh Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09:00 na daren ranar Litinin inda ƴan fashin daji suka fito daga cikin dai-dai kan wata kwana inda suka buɗe kan motar mai cin fasinjoji 18 da ta ɗauko su  daga Abuja zuwa Kaduna.

Ƴan bindigar sun harbin tayar motar abun da ya tilastawa motar shiga cikin daji kana daga bisani suka tasa ƙeyar fasinjojin ya zuwa cikin daji.

Ya ƙara da cewa an kuma tasa ƙarin wasu fasinjojin daga wasu motoci biyu ya zuwa cikin daji.

Ya cigaba da cewa abun haushin shi ne wurin da lamarin ya faru ba shi da nisa da shingen binciken da sojoji suka saka.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...