Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mata 8 Abuja

Wasu mata 8 ne aka yi garkuwa da su dai-dai lokacin da suke aiki a wata gona dake kauyen Gwombe dake ƙarƙashin masarautar Gwargwada a karamar hukumar Kuje ta birnin tarayya Abuja.

Sace matan na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan da wasu yan bindiga suka sace mahaifin mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali tare da wasu mutane 6 a kauyen Yawuti dake karamar hukumar Kwali dake Abuja.

Wani mazaunin Gwargwada, Usman Yakubu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin.

Ya ce matan dukansu matan aure ne kuma ƴan bindigar ɗauke da bindigar AK-47 sun kewaye su a cikin gonar kana suka yi awon gaba da su.

Wani mai riƙe da sarautar gargajiya a ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce huɗu daga cikin matan sun fito ne daga gida guda.

More from this stream

Recomended