Ƴan Bindiga Sun Sace Wani Babban Limami

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace Ibrahim Bodunde Oyinlade babban limamin garin Uso dake karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Kamfanin Dilllancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa an sace limamin mai shekaru 67 a gonarsa dake sansanin Asolo da tsakar ranar Asabar.

Wata majiya dake iyalinsa ta ce sun kai rahoton bacewarsa gurin yan sanda bayan da ya kai ƙarfe biyu bai dawo gida ba kuma wayarsa ba a daga wa.

“Masu garkuwar sun tuntubi iyalinsa amma har yanzu basu bukaci kuɗin fansa ba,”ya ce.

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, Olufunmilayo Odunlami-Omisanya mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta ce yan sanda da kuma yan bijilante suna bincike dazuka don neman limamin.

Odunlami ta ce an gano waya da kuma motar limamin a gonar.

More from this stream

Recomended