Ƴan bindiga sun kashe wani lauya

Ƴan bindiga sun kashe wani matashin lauya,Barista Mike Ofikwu  a garin Otukpo dake jihar Benue.

Mazauna garin sun ce matashin lauyan dake fafutukar kare hakkin jama’a an buɗe masa wuta an har sai da ya mutu ranar Laraba da daddare a kusa da gidansa dake kan  layin Otukpa a garin Otukpo.

Wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga biyu ne suka farmasa a ƙofar gida inda suka buɗe masa wuta.

An kuma garzaya da shi asibitin dake kusa inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended