Ƴan bindiga sun kashe mai POS a Ekiti

Wasu ƴan bindiga sun kashe wani mai sana’ar POS a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti.

Mai sana’ar ta POS dake da suna Alfa Taofeek an harbe shi ne a shagonsa dake wajen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa ƴan bindigar sun isa shagon marigayin akan babur inda suka buɗe masa wuta suka tsere da kuɗaɗen da ba a san adadin su ba.

Taofeek ƙaramin fitaccen ɗan kasuwa ne abin da ya sa ko da yaushe akwai kuɗaɗe a hannunsa saboda yanayin kasuwancinsa.

Babu jimawa kaɗan ƴan bindigar sun sake harbe wani mutum mai sayar da shinkafa a kasuwar Bisi dake Ado-Ekiti.

Abun da ya tilastawa ƴan kasuwa da masu sayayya tserewa da ƙafafunsu.

Abutu Sunday mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Ekiti ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce kawo yanzu ba a kama waɗanda suka aikata kisan ba sai dai tuni rundunar ta baza komarta.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...