Wasu ƴan bindiga da suka fito daga Najeriya sun kashe a ƙalla sojojin ƙasar Kamaru biyar a ƙauyen Bakinjaw dake kan iyakar ƙasashen biyu.
Aka Martin Tyoga wani ɗan majalisa dake wakiltar gundumar ya faɗawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Asabar cewa harin ya faru da tsakar daren ranar Alhamis lokacin da Fulani ɗauke da makamai daga jihar Taraba suka tsallaka suka kai hari kan wani sansanin sojoji.
Tyoga ya ce harin na ramuwar gayya ne bayan da sojojin ƙasar ta Kamaru su ka kashe Fulani da dama kwana ɗaya kafin harin.
Agwa Linus basaraken gargajiya na Bakinjaw ya ce maharan sun ƙona fadarsa a lokacin harin.
Ya ce wannan ba shi ke karo na farko ba da suke kai harin.